Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobara Ta Kona Wani Sashi Na Matatar Man Dangote


Matatar Man Dangote
Matatar Man Dangote

Da safiyar Laraban nan ne aka wayi gari da samun tashin gobara a matatar man fetur ta Dangote a jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Ko da yake kokarin jin ta bakin masu magana da yawun kamfanin na Dangote yaci tura, sai dai a wata wasika da bangaren hulda da jama’a na kamfanin Dangoten ta aikawa ‘yan jaridu na cewa, gobarar wadda aka kashe ta tun da sanyin safiya bata yi illa ga kamfanin ba kuma babu wani ma’aikacin kamfanin da ya samu rauni.

Mai magana da yawun kamfanin Anthony Chiejina ya ce hukumomin kamfanin na gudanar da bincike a halin yanzu.

Wannan gobara ta auku ne a daidai lokacin da ake cacar baka tsakanin kamfanin na Dangote da manyan kamfanonin samar da mai na kasa da kasa da kamfanin Dangoten ya zarga da yi masa zagon kasa, wajen hana shi sayen danyen mai, lamarin da ke sanya shi zuwa kasar Amurka domin sayen danyen mai da zai sayar a ciki da wajen kasar.

Matatar Man Dangote
Matatar Man Dangote

Wani masanin tattalin arziki da saka jari, Dakta Dauda Muhammed Kontagora, ya shaida wa Muryar Amurka cewa, irin wannan gobara zai sa masu saka jari yin dari-dari da shiga Najeriya kuma hakan na iya sanya jama’a zargin zagon kasa ga kamfanin cikin gida da ‘yan kasar ke ganin sa a matsayin abin koyi.

Ya kara da cewa dole ne hukumomi su tashi tsaye wajen marawa kamfanonin cikin gida baya domin hakan ne zai saka kasar ta zama mai dogaro da kai, da bunkasa tattalin arziki da kuma saka jari a zahiri.

A zamanin tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne dai aka kaddamar da matatar man Dangote, ko da yake bai fara aiki ba gadan-gadan, sai a kwanan nan tare da sarrafa man fetur na Diesel dana jiragen sama.

Har yanzu matatar bata fara sarrafa man fetur na ababen hawa ba, balle sayarwa a cikin gida, abun da kuma masana ke ganin na cikin matsalolin da matatar ke fuskanta daga gwamnati dama kamfanonin kasa da kasa da su ka yi kaka gida a harkokin mai a Najeriya.

'Yan Najeriya dai suna saka rai da zarar matatar man ta Dangote ta fara aiki watakila farashin man fetur da ya yi tashin gauran zabi zai dan sauko.

Sai dai masana na ganin ba lallai farashin ya sauko ba kamar yadda mutane ke tsammani.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG