Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar: Majalisar Dokoki Ta Yi Watsi da Bukatar Gurfanar da Shugaban Kasa


Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar
Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar

Majalisar dokokin jamhuriyar NijAr ta yi watsi da takardar da ‘yan adawa suka shigar a makon jiya akan bukatar gurfanar da shugaba ISUHU MAHAMADU da suke zargi da rufe ido akan wasu laifufkan da suka hada da batun kudaden nan da aka kama a hilin jiragin saman JORI HAMANI yayinda wasu ke shirin fita da su ta barauniyar hanya amma aka yi umurnin a mayar masu abinsu.

A karshen wani taron nazarin wannan bukata ta gurfanar da shugaba ISUHU MAHAMADU ne kwamitin gudanarwar majalisar dokokin kasar ya gano rashin dacewar hanyoyin da ‘yan adawa suka bi a yayin ajiye takardar a gabanmajalisar sakamakon lura da cewa yunkurin na ‘yan hamayyar ya sabawakundin tsarin mulkin kasa da ka’idodin majalisar kamar yadda dan majalisar dokokin kasa na bangaran rinjaye ALHAJI SHAFI’U MAGARYA ya min bayani. Ya kara da cewa ana barin halak da kunya.

Sai dai a ra’ayin ‘yan adawa masu rinjaye anfani ne suka yi da karfin mulki domin watsi da wannan bukata ta ladabtar da shugaban kasa inji TIJANI ABDUKADRI jagoran ‘yan majalisa na ARN.

A dai wani bangaren wata kotun Yamai ta sallami mutanen da aka kama a ranar da tsohon kakakin majalisar dokokin kasa Hamma Amadu ya dawo Nijar in ban da wasu kusoshin jam’iyar Moden Lumana su 4 da aka aika gidan yarin dake yammacin birnin Yamai cikinsu har da SUMANA SANDA bisa zarginsu da laifin furta kalaman da ka iya tunzura jama’a.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:03 0:00
Shiga Kai Tsaye

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG