Ina sayan shinkafar gwamnatin buhu-buhu domin sayarma ma’aikata a ma’aikatun gwamnati daban-daban, domin su biya a karshen wata, duba da ganin cewar kananan sana’o'i da mata kan yi a gidajen su yana karewa ne a bashi.
Wata matashiya malama Sa’adatu Hassan, ce ta bayyana haka yayin da take zantawa da wakiliyar DandalinVOA, Baraka a birnin Kano. Tace da ta sami karamin jarin, sai tayi tunanin wacce sana’ace zata yi ta fita ba tare da an rike mata kudade ba, sai ta lura da cewar shinkafa na daya daga cikin abubuwan da ake bukata a kullun, inda ta fara da buhu shida tana kaiwa ma’aikatun gwamnati.
Sa’adatu, ta ce babban matsalar da mata ke fuskanta shine rashin tunanin mai zurfi kafin su fara sana’a, tare da jan hankalinsu cewar ya kamata su daina raina jari ko kudin da suka samu, ta hanya samun wata sana’ar da zai kai su ga mafita.
Ta ce mata su daina raina karamin jari domin a cewarta suna iya habbaka idan an bidasu ta harkar kasuwancin da ya kamata, da zummar bunkasa zuwa babban jari, inda take cewa kamar ita ta fara ne da buhu shida, wanda a yanzu haka tana sayar da buhun shinkafa kimanin 20, ga ma’aikata da suke biya a duk karshen wata da zarar anyi albashi.
Ta kara da cewa babban burinta ta zama hamshakiyar 'yar kasuwa da take sayar da shinkafa.
Facebook Forum