Na yi karatun gaba da sakandare a jihar Borno duk da cewar a lokacin da nake karatun matsalar ‘yan Boko haram bata kankama ba wanda hakan bai kawo tsaiko ga harkar karatuna ba inji matasahiya Malama Fatima Gambo Abubukar.
Ta bayyana haka ne a yayin da take zantawa da wakiliyar DandalinVOA Baraka Bashir, inda ta ce a lokacin da take karatunta masu tada kayar baya basa taba fararen hula, don haka babu wata razana ko fargaba, duk da cewa ta taba yin tozali da su a yayin da take dawowa daga wata unguwa.
Matashiyar ta kara ca cewa ta karanci harkar jarida ne, a cewarta domin tana so ta bada tata gudunuwar wajen wayar da kan al’umma kan wasu batutuwa da ke damun al’umma.
Fatima Gambo ta ce ta yi rayuwar maraici amma ‘yan uwanta sun taimaka mata wajen tabbatar da ta sami damar yin boko, domin cimma burinta na rayuwa, kuma tayi aiki a jihar Borno, kafin daga bisani yanayin rayuwa a jihar da aiki ya tilasta ta barin aikin.
Ta ce burinta dai bai wuce ta cigaba da wayar da kan mutane kamar yadda kowane dan jarida ke fata ba, inda ta ce zuwan kafafan yada labarai ya wayar da kan al’umma sosai ta fannin sanin ‘yancinsu.
Facebook Forum