Gwamnatin jihar Kaduna ta gano Naira miliyan 120, da ma’aikatan boge ke waskewa a jihar Kaduna aduk wata.
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiri El-Rufai, ya kuma kara tabbatarwa da ma’aikatan jihar cewa a wannan watan ma sai an tantancesu kafin su karbi albashinsu.
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi wajen taron jin ra’ayoyin aluma da aka gudanar a Zaria.
Malam El- Rufai, ya kara da cewa”An yi bincike na farko Naira milyan 120,da ake sacewa watan da ya wuce muka hana satan amma ba’a gama ba domin har yanzu muna da masaniya domin mutane suna aiko mana a wuri kasa wane da wane ba ma’aikata bane amma suna karban albashi, wane yam utu amma har yanzu ana karbar albashin shi, akwai likitoci guda biyu a wani asibiti anan jihar Kaduna wadanda suna aiki a Abuja, kuma suna karban albashi a Kaduna, toh duk wadannan abubuwa muna da masaniyarsu saboda haka mun sake duba tsarin da aka yin na watan daya wuce zamu gyara shi za’a sake yi wannan watan kuma yanzu idan za’a sake yi bawai kawai zaka zo da takardun na aiki, zamu fito da sabon tsari wanda akwai dan Sanda da ankwa yana jiran ka idan kazo aka gane karya kake sai a samaka ankwa a kai ka inda ya kamata.”
Yana mai cewa” Mun je makarantar Alhudahuda dake Zaria munga ginin da akayi a filin makaranta kuma ranar laraba wa’adin shi zai cika bayan laraba duk abunda ya samu wanda yake ciki shi ya jawo wa kansa.”
Daya daga cikin mahalarta wannan taro yaso da wani uzuri game da yunkurin ruguje gidajen da Gwamna Nasiru El- Rufai ke niyyar yi, yana mai cewa a ka’idar Musulunci wanda ya kwaci fili ya saidawa wani shi zai biya mai filin na shi kuma mai filin nan a rusa.