Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nemama Falestinawa Yanci ya Shafi Dukkan Al’uma Inji El-Zazzaky


QUDUS
QUDUS

Rikicin Falestinawa da Yahudawa ya samo asalin ne daga nuna wariyar dangantaka, wato ma’ana Yahudawa nanu dafkar Falestinawa basu da hurumin sama a yankunan nasu.

Imam Muhammad Al’asi, daga Washington ta kasar Amurka, ne ya furta haka a wajen taron Qudus da ‘yan uwa Musulmi, ta Najeriya, ta shirya a Abuja, yace kimanin Falestinawa miliyan arba’in da biyar ne suka yi gudun hijira daga yankin kuma basu da ikon dawowa saboda wannan banbancin.

Malamin ya ci gaba da cewa dan yadda fasarar Tsohon Alkawari da Attaura na nuna wariya yasa tafkar Falestinawan ma sun zama abun kyama da hakan ya zama wajibi ba wai kawai a kwatowa Falestinawan yankin nasu ba, har ma sai an sauya tunanin Yahudawa da yadda suke ganin sun fi kowa daraja a duniya.

Sheikh Ibrahim El Zazzaky, na ganin nema ma Falestinawa yanci ya shafi dukkan al’uma, yana mai cewa idan kwacen hakin wani ya zama daidai toh shi wannan ba kwacen Falestinu ba kowane kwace ma zai zama daidai.

Wani mai bishara na mabiya addinin Kirista, Pastor Yohanna Buru, daga Kaduna da ya halarci8 taron na ganin fushin Allah ne ya shafi Yahudawa tun taurine kai da suka yiwa Annabi Musa, baya Allah ya cece su daga Firauna.

Mai bisharan ya kara da cewa “ matukar baku bi ummarnina tun daga farko ba zai bar Falestinawa a cikin kasar kuma zasu zame maku karfen kafa.

XS
SM
MD
LG