‘Dan wasan Barcelona Neymar ya fada cewa shi ba wai yana kokarin wuce takwaransa Lionel Messi ba, domin zama zakaran ‘dan wasan duniya.
Cikin shekaru shida da suka wuce Lionel Messi ke zama gwanin ‘dan wasan duniya har sau hudu, amma wannan shekarar Neymar ya shiga sahun da zai kalubalanci Messi kan neman wannan matsayi.
A ta bakin Neymar alokacin da yake magana da gidan talabishin na SporTV yace, “ba niya ta bace na nayi kokarin wuce Messi ba.”
Ya cigaba da cewa ina kokarin kawai naga na sami ci gaba a rayuwata, ina kuma son na ci gaba da yin abinda na saba, domin samun zama zakara dama burin rayuwa ta.
Neymar da Messi zasu zamanto a bangare dabam dabam alokacin da kasar Brazil zata kara da Argentina, a wasan neman shiga wasan cin kofin duniya na shekara ta 2018, Neyamar dai yayi alkawarin taimakawa kasar sa wajen samun nasarar wasan.
Neymar dai yace Messi babban ‘dan wasa ne, kuma ba abune mai kyau ba a kara da shi, amma kuma ba hamtaccen abu bane. Ya kuma ce zai yi duk abinda ya dace wajen ganin sun sami nasara akan Brazil.
Brazil dai zatayi wasannin ta na farko da Chile da Venezuela ba tare da Neymar ba, a dalilin jan katin da ya samu a wasan Copa America.