Yunkurin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, na ganin an sake bude ayyukan jigilar fasinjoji na kasa-da-kasa a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano, da filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ake cigaba da aiki a kai don bunkasar tattalin arzikin jihar Kano, ya kusa yiwuwa.
Shi ma, Ministan sufurin jiragen saman Najeriya, Hadi Sirika, ya bayyana cewa, tattaunawa a kan sake bude zirga-zirgar kasa da kasa a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano, da sabon filin jirgin saman kasa-da-kasa na Murtala Muhammad, ta yi armashi.
Game da batun ba wa masu zuba jari daga ciki da wajen Najeriya damar shiga a dama da su, wajen bunkasa fannin sufurin jiragen saman Najeriya, Sirika ya ce. "Wannan gwamnatin ba za ta saida kaddarorin al'umma ba, kamar yadda aka yi a baya, za dai a bada su a matsayin jingina, a kuma bunkasa su, daga baya su kuma cigaba da zama mallakar kasa."
Sake bude zirga-zirgar jirgin saman kasa da kasa a Kano zai yi matukar tasiri ga tattalin arzikin Najeriya in ji Jamil Yunusa. "musamman idan aka yi la'akari da irin hada-hadar da ake samu a jihar."
Ga rahoton Halima Abdulra’uf a cikin sauti.