Babban Darakta a hukumar Garba Abari, ne ya bayyana hakan yayin da yake nuna gamsuwarsa da jawaban shugabanin hadaddiyar kungiyar fatake ta Najeriya, saboda matakin janye yajin aikin da suka yi a baya-bayan nan.
"Ya kamata a kowane lokaci idan abu irin wannan ya faru, a samu dama a rika yin bayani, domin rashin bayani na haifar da al'amura da dama," Abari ya ce a Taron Zauren VOA da ake yi wata-wata a Abuja.
Karin bayani akan: Dakta Muhammad Tahir, NOA, Nigeria, da Najeriya.
Kungiyar masu safarar kayan abinci na Najeriya sun tsunduma yajin aiki a makon da ya gabata, lamarin da ya haifar da hauhawar farashin kayan masarufi a kudancin Najeriya da kuma karancin kasuwar kayayyakin a arewaci.
Kungiyar ta nemi gwamnatin tarayya ta biya ta diyyar mambobinta da aka kashe da kuma dukiyoyinsu da aka lalata a lokacin rikicin Ensars da na Sasha.
Shugaban hadakar kungiyoyin fataken ta Najeriya, Dakta Muhammad Tahir, ya yi karin haske kan matakin janye yajin aikin kai kayan abincin zuwa duk sassan na Najeriya, ya na mai cewa, suna kan tantance asarar da mambobinsu suka yi don neman diyya.
A nasa bangaren, shugaban hadakar kungiyoyin fatakan na Najeriya, reshen jihar Legas, Haruna Muhammad, ya ce ba matsalar da mambobin kungiyar su ke fuskanta bayan janye yajin aiki illa na karbar kudadden harajin bogi a hanyoyi, yayin fataucin ba bisa ka’ida ba.
Shi ma mataimakin shugaban kungiyar ‘yan kasuwan arewacin Najeriya, Adam Ibrahim, ya bayanna tasirin yajin aikin fatakan ya yi ga sauran al’umma ban da ‘yan kasuwa.
Martin Igwe da ke zama jagorar ayyuka na daya daga cikin kungiyoyin zaman lafiya a Najeriya, ya ce kaya sun kara kudi a yankunan kudancin kasar.
A ranar 25 ga watan Febrairun ne hadakar kungiyoyin fatakan ta Najeriya ta fara yajin aikin gamagari wanda kungiyar ta janye bayan shiga tsakani da gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya yi a madadin shugaban kasar Najeriya kwanaki uku da suka gabata.
Ga rahoton Halima Abdulra’uf a cikin sauti.