Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abin Da Sarkin Kano Ya Ce Kan Matsalar Tsaro a Jawabinsa Na Cika Shekara a Kan Karagar Mulki


Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya cika shekara guda da hawa karagar sarautar Kano, bayan sauke tsohon sarki Muhamamdu Sanusi na biyu.

Mai Martaba Alhaji Aminu Ado Bayero da ke zaman Sarkin Kano na 15 a jerin Sarakunan Fulani, ya hau gadon sarautar Kano a ranar 9 ga watan Maris na bara, bayan tunja-tunjar da ta kai ga tunbuke tsohon sarki Muhamamdu Sanusi na biyu daga karaga.

A cikin jawabinsa Sarki Aminu Ado Bayero ya ce duk da kalubalen da ake fuskanta kamar na annobar cutar Coronavirus, matsalar tsaro da fadiwar tattalin arziki ya ce ya cimma farfado da aminci tsakanin masarautar Kano da sassan gwamnati da na masarautu a jihar baki daya.

Karin bayani akan: Kano, Boko Haram, Sarki Aminu Ado Bayero, Nigeria, da Najeriya.

Sarkin ya kara da cewa an samu daidaito tsakanin Gwamnatin jihar da masarautar, kuma sun kai ziyara don kara dankon zumunci ga masarautun jihar da na wasu na Arewacin Najeriya.

Sarkin na Kano ya ja hankalin talakawa dangane da kalubalen tsaro da ya addabi Arewacin Najeriya, ya ce su yi hattara akan abubuwan da ke faruwa.

Sannan kuma ya shawarci gwamnatoci game da halin da kasa ke ciki.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga gwamnatin tarayya da ta bullo da hanyoyin sana’o’i da na noma domin taimakawa talakawa musamman matasa dake zaune ba su da ayyukan yi.

A Najeriya matsalar tsaro ta yi kamari musamman a arewaci inda garkuwa da mutant domin neman kudin fansa da hare-haren 'yan bindiga suka zama ruwan dare.

Wannan na faruwa ne baya ga matsalar Boko Haram da ta addabi arewa maso gabashin Najeriya.

Gwamnatin tarayya ta ce tana iya bakin kokarinta, wajen ganin ta shawo kan wadannan matsaloli.

A saurari rahoto cikin sauti daga Mahmud Ibrahim Kwari:

Abin Da Sarkin Kano Ya Ce Kan Matsalar Tsaro a Jawabinsa Na Cika Shekara a Kan Karagar Mulki
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG