Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Najeriya Sun Bayyana Damuwa Kan Ware Naira Bilyan 797.2 Don Sake Shimfida Hanyar Abuja-Kaduna-Kano


Ana gayran hanya
Ana gayran hanya

Bayan amincewar majalisar zartarwar Najeriya kan ware Naira biliyan 797 da milyan 200 don sake shimfida hanyar Abuja zuwa Kaduna da Kano, ‘yan kasar sun fara bayyana damuwa kan yadda aka saba ware makudan kudadde don gyara a baya kuma ba a gani a kasa.

Suna bayyana fargaba ne saboda gudun kar a sake komawa gidan jiya kan gina hanyoyin, duba da yadda a baya aka gudanar da aikin da ya yi saurin lalacewa.

Damuwar ‘yan Najeriya kan aikin sake shimfida titin Abuja zuwa Kaduna da Kano dai, da aka ware wa tsabar kudi na Naira biliyan 797 da milyan 200 shi ne bibiyar aikin don tabbatar da cewa an yi yadda zai dade bai lalace ba kamar yadda, Suleiman Abdul, da ke yawan tafiye tafiye daga Kaduna zuwa Kano da Abuja, ya bayyana.

Ya ce gyarar da aka ce ana yi kan hanyar Abuja zuwa Kaduna da Kano, ba su ga komai na faruwa daga Abuja zuwa Kaduna ba, sai dai daga Mararrabar Jos da Zaria da gadar Kawo kadai suka ga ana wasu ayyuka. A dan haka ya yi kira ga gwamnati da ta rika bibiyar aiki idan ta bada kwangila saboda rashin yin haka na kawo matsaloli.

Ministan Ayyuka, Babatunde Fashola, shi ne ya bayyana cewa, majalisar zartarwar ta amince da batun sauya fasali na sake shimfida titunan da abin da zai biyo baya na sauya farashin aikin a yayin taron na ranar Laraba, wanda kudin da ta amince a yi aiki da shi ya zarta na gyarar titunan da aka amince da shi a baya na Naira bilyan 155 da Naira biliyan 642 da milyan 200.

Masani a sha’anin tattlin arziki, Yushau Aliyu, ya yi bayani a kan tasirin da sake shimfida titunan zai yi ga ‘yan kasuwa da ke fataucin kayayyaki wanda zai bunkasa tattalin arzikin kasar muddin wadanda nauyin aikin ya rataya a wuyarsu ba su wawure kudadden ga biyan bukatu na kansu ba.

Idan ba a manta ba a shekarar 2017 ne gwamnatin Najeriya ta ba wa kamfanin Julius Berger kwangilar aikin gyarar titin Abuja Zuwa Kaduna da Kano, aikin aka yi ta samun jinkiri a kai ya zuwa lokacin da majalisar zartarwar kasar ta amince da batun sake shimfida titunan.

Ga dai rahoton Halima Abdulra’uf daga birnin Abuja a Najeriya:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00
XS
SM
MD
LG