Shugaban hukumar jiragen saman kasar ta FAAN, Captain Rabiu Yadudu, ya ce tuni da aka cika umarnin na gwamnati, ta hanyar kara jami’an tsaro da matakan shiga, kazalika da tsaron ma’aikata a filin jirgin na Kaduna da sauran filayen jiragen Arewacin Najeriya.
A ranar Juma’a ne da dare, wasu ‘yan bindiga suka suka kai hari a gidajen ma’aikatan filin jirgin na Kaduna, inda rahotannin suka bayyana cewa sun yi awon gaba da mutane 9, da suka kumshi ma’aikatan filin jirgin da kuma wasu iyalansu.
Rahotannin sun bayyana cewa maharani sun sami shiga gidajen ma’aikatan ne ta hanyar babban titin gudun fanfalaki na filin jirgin, inda kuma suka kai har safiyar Assabar suna gudanar da farmakin na su.
Yadudu ya ce jami’ansa na aiki tare da jami’an tsaro da kuma gwamnatin jihar Kaduna domin ganin an sako mutanen da aka sace, inda ya ce tuni da ayarin suka soma tattara bayanan sirri na ganin an samo hanyar magance sake aukuwar irin wannan lamarin.
Ya kara da cewa rahoton bincike akan irin wannan harin da aka taba kaiwa a bara, ya kara taimaka musu wajen tsara matakan tunkarar irin wannan kalubalen.
Shi kuwa shugaban hukumar sararin samaniya ta Najeriya (NAMA), Captain Fola Akinkuotu, ya bayyana damuwa akan cewa fiye da sao’i 24 bayan sace mutanen, ‘yan bindigar ba su tuntubi hukumar ko wasu makusantan ma’aikatan ba.