Niamey, Niger —
A shirin da ya gabata mun sami bakuncin darektar wata makarantar faramari a birnin konni dake jihar Tahoua Jamhuriyar Nijer, Madame Ado Zeinabou Abdallah wace ta fara da yin bayani a game da yadda aka yi ta tsinci kanta cikin halin gurgunta da ma abinda ya shafi dangantakar ta da sa’oin ta na ajin makaranta. To a yau a ci gaban hirarsu da wakilin sashen Hausa Harouna Maman Bako, bakuwar shirin ta fayyace irin fafitikar da ta sha kafin ta sami kai wa ga cimma gurinta na zama malamar makaranta kasancewar a wancan lokaci an jahilci amfanin ilimin nakasassu.
Saurari cikakken shirin: