Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya tana shirin kwashe mutanenta daga Libya


Shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan.
Shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan.

Gwamnatin Najeriya tace zata kwashe mutanenta daga Libya, yayinda gwamnatin tayi Allah wadai da yadda shugaban kasar Libya Moammar Gadhafi yake amfani da karfi wajen murkushe masu zanga zanga

Gwamnatin Najeriya tace zata kwashe mutanenta daga Libya, ta kuma yi Allah wadai da yadda shugaban kasar Libya Moammar Gadhafi yake amfani da karfi wajen murkushe masu zanga zanga. Ministan harkoki kasashen ketare Odein Ajumogobia yace shugaba Goodluck Jonathan ya kuduri aniyar daukar matakan da suka wajaba wajen tabbatar da tsaro da lafiyar ‘yan Najeriya dake kasashen ketare.Bisa ga cewarshi, shugaban kasar ya bada umarnin kwashe fasinjoji ‘yan Najeriya da suka rasa gaba ko baya a biranen Tripoli da kuma Benghazi kamar yadda aka yi a birnin Alkahiya. Ajumogobia yace yana tattaunawa a kai a kai da jami’an diplomasiya a arewacin Afrika yana kuma sa ido kan abubuwan dake faruwa a Algeriya da Misira da kuma Libya. Ministan yace za a iya warware takaddamar ta wajen tattaunawa da dukan wadanda abin ya shafa, tare da shawartar gwamnatin kasar Libya ta saurari jama’arta. Ajumogobia yace gwamnati ta riga ta shawarci jakadanta su kwashe iyalansu yadda jami’an diplomasiyan zasu iya maida hankali kan aikin dake gabansu. Da wannan yunkurin Najeriya ta shiga sahun sauran kasashen duniya inda kafar sadarwar kasar China tace gwamnatin kasar tana shirin kwashe kimanin ‘yan asalin kasar dubu talatin da uku dake Libya yayinda kasar Bangladash kuma ke neman tallafin kasa da kasa wajen kwashe mutanenta dubu sittin.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG