Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Gadhafi ya yi gargadi da cewa kasar zata iya shiga yakin basasa


Dandazon masu zanga zanga yayinda hayaki ya turnuke wani gini da aka ce shelkwatar harkokin tsaron cikin gida ne a birnin Benghazi
Dandazon masu zanga zanga yayinda hayaki ya turnuke wani gini da aka ce shelkwatar harkokin tsaron cikin gida ne a birnin Benghazi

Kazamar zanga zangar kin jinin gwamnati ta bzau a Tripoli babban birnin kasar Libya

Kazamar zanga zangar kin jinin gwamnati ta bazu a Tripoli babban birnin kasar Libya, yayinda dan shugaban kasa Moammar Ghadafi ya shaidawa mutanen kasar a wani jawabi da aka yayata a tashar talabijin cewa, kasar zata tsunduma cikin mummunan yakin basasa idan suka hambare mahaifinsa da ya shafe shekaru 40 bisa karagar mulki. A wani jawabi da yayi da asubahin yau Litinin, Saif al-Islam Gadhafi ya yi gargadi da cewa, kogin jini zai cinye arzikin mai na kasar, ya maida kasar karkashin mulkin mallaka idan har aka gaza shawo kan lamarin. Ya zargi’yan kasar Libya dake gudun hijira, da ‘yan kishin Islama da kuma kafofin sadarwa na kasashen ketare da ‘yan kwaya da kuma masu aikata miyagun laifuka da haddasa tashin hankalin, ya kuma yi ta jadada cewa, Libya ba Masar bace ba kuma Tunisiya ba ce, kasashen dake makwabtaka da aka hambare shugabanninsu kwanan nan. Ya bayyana kasar Libya a matsayin kasar kabilu dake cike da makamai wadda nan da nan zata iya tsunduma cikin yakin basasa. Gadhafi ya yi wani kwarya kwaryan tayin garambawul da ya hada da tattaunawa kan kundin tsarin mulkin kasar da kuma sabon tsarin gudanar da harkokin mulki. Sai dai jawabin nashi ya fi bada karfi kan yiwa ‘yan kasar Libya barazanar rudami.

XS
SM
MD
LG