Shugaban kasar Libya Moammar Gadhafi yace zanga zangar kin jinin gwamnatin da ake yi a kasar ba zata tilasta mashi barin mulki ba, bisa ga cewarshi ya gwammace ya yi mutuwar shahada a Libya.
Mr. Gahdafi ya yi Magana a tashar talabijin ta kasar Libya jiya Talata a jawabinsa na farko da ya yi ga kasar tunda aka fara zanga zangar da aka zubar da jini. Ya yi kira ga magoya bayansa su taimaka wajen kare kasar Libya daga mutanen da ya kira “yan daba” da kuma “yan ta’adda”.Mr. Gadhafi da ya rike wani koren littafin da ya yi kama da taswirar tsarinshi na siyasa, ya yi barazanar zartar da hukuncin kisa kan duk wanda ya kaiwa Libya hari ko kuma ya aikata leken asiri.
Jiya Talata har wa yau, wani abokin huldar Mr. Gadhafi na kusa, ministan harkokin cikin gida Abdel Fattah Younis, ya sanar da yin murabus da kuma goyon bayan juyin juya halin ranar 17 ga watan nan na Fabrairu.Da yake magana da tashar Al jazeera daga birnin Bengazi inda ake zanga zangar, Younis ya yi kira ga rundunar soji ta marawa mutanen baya wajen neman biyan bukatunsu.
Manyan jami’an kasar Libya da suka hada da ministoci da jami’an diplimasiya da jami’an sojoji sun watsar da gwamnatin suka sanar da goyon bayan tawayen. A halin da ake ciki kuma wani jami’in Majalisar Dinkin Duniya yace wata ma’aikaciyar cibiyar a Libya ta ga jirage masu saukar angulu suna shawagi sai dai bata tabbatar da kai hari kan farin kaya ba. Lynn Pasco da take magana a birnin New York, tace Majalisar Dinkin Duniya tana kyautata zaton an keta kadin bil’adama a kasar dake arewacin Afrika kuma lamarin yana kara muni.
Jakaden Libya a Majalisar Dinkin Duniya yace rundunar mayakan saman kasar bata kaiwa farin kaya hari ba, sai dai ya tabbatar da cewa,galibin lardin gabashin kasar yana karkashin dakarun dake kin jinin gwamnati. Abdurrahman Shalgham ya kuma ce babban mai shigar da kara na kasar Libya ya fara gudanar da bincike kan mutuwar masu zanga zangar.
Shaidu a birnin Tripoli sun ce jiragen yaki masu saukar angulu da manyan jiragen yaki sun kai hari kan wani yankin farin kaya ranar Litinin, yayinda sojojin haya ‘yan kasar Afrika da ‘yan bindiga magoya bayan Gadhafi suka rika harbin kan mai uwa da wabi da nufin razana jama’a.
Kungiyar Human Right Watch tace ta sami rahotannin mutuwar a kalla mutane 62 a Tripoli daga ranar Lahadi, banda adadin mutane 233 da ta samu tun farko, akasarinsu daga lardunan gabashin kasar.