Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Harin Da Aka Kai A Yankin Tsakiyar Nijeriya Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutane Hudu


'Yan sandan kwantar da tarzoma na Najeriya
'Yan sandan kwantar da tarzoma na Najeriya

‘Yan bindiga sun kashe mutane hudu a kalla a kusa da garin Jos, wanda ya a ‘yan shekarun nan ya zama dandalin rikicin addini akai-akai.

‘Yan bindiga sun kashe mutane akalla hudu a kusa da garin Jos, wanda ya a ‘yan shekarun nan ya zama dandalin rikicin addini akai-akai.

Shaidu sun ce da talatainin daren jiya maharan su ka afkawa wani kauye a bayan garin Jos.

Birgediya-Janar Hassan Umaru, wanda ke shugabantar rundunar sojojin Najeriya na musamman da aka girke a yankin, ya gayawa manema labarai cewa mutane hudu aka kashe, amma mazauna kauyen sun ce wadanda su ka mutu sun fi hudu.

Shekaru da dama kenan da garin Jos da sauran wuraren da ke kewayen jahar Plateau ke fama da rikicin Musulmi da Kirista wanda ya samo asali daga gwagwarmayar neman ikon siyasa da na tattalin arziki.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG