Majalisar Dokokin Jihar Zamfara Ta kara wa'adin shugabannin Kananan Hukumomi, Amma Da Magana |
Majalisar dokokin jihar Zamfara ta kara wa'adin shugabannin kananan hukumomin jihar su 14 bayan wa'adin shugabancinsu na yanzu ya kare cikin wadan Febwairu da ya shude ranar litinin. Majalisar ta kara wa'adin ne har na tsawon wata hudu.
Amma kamar cikin wasan kwai-kwayo,wasu wakilan majalisar dokokin jihar sun tsame hannunsu daga wan mataki suna zargin cewa,majalisar ta sabawa dokar mulkin kasa,kuma sai da aka basu cin hanci kamin su dauki wan nan mataki.
A wani taron manema labarai da suka kira a birnin Gusau ranar litinin,dan majalisa Ibrahim Kulchin-Kalgo yayi zargin cewa,shugaban masu rinjaye, Alhaji Mani Mallam Mummini ya karbo kudi cin hanci daga shugabannin kananan hukumomin su 14 ta hanun shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomi, Alhaji Umaru Jibo,wanda shima shugaban karamar hukuma ne domin a kara musu wa'adi.
A taron manema labarai Alhaji Ibrahim Kalgo ya yi zargin shugaban masu rinjaye ya kawo musu kudi Naira milyan 15 domin su amince da wan nan kuduri. Ga rahoto da wakilinmu dake Gusau ya aiko mana.