Wata babbar kotu a Nijeriya ta yanke hukuncin cewa gwamnonin jihohi biyar na jam’iyya mai mulki, ba su bukatar shiga zaben watan Afirilu don wa’adinsu bai kare ba.
Hukuncin da kotun ta yanke a jiya Laraba ya shafi gwanonin jihohin Bayelsa da Cross River a yankin Niger delta mai arzikin man fetur, da kuma jihohin Kogi da Adamawa na yankin tsakiyar Nijeriya da kuma Sakkwata ta arewa mai nisa.
Alkali Adamu Bello na Babbar kotun tarayya da ke Abuja ya ce hukumar zabe ba ta da ikon gudanar da zabe a jihohi biyar din har sai bayan kwanaki 60 da karewar wa’adin gwamnonin na yanzu.
Wannan kasar da ta fi yawan jama’a a Afirka, za ta gudanar da zabe a watan Afirilu na shugaban kasa da gwamnoni da ‘yan Majalisa.