Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NAJERIYA: Shugaba Buhari Ya Kori Shugabannin Sojoji Ya Nada Wasu Sabbi


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari'
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari'

Yau Litinin 13 ga watan Yuli shugaban kasar Najeriya Muhammad Buhari ya kori shugabannin sojoji ya kuma nada wasu sabbi da suka maye gurbinsu

A zantawar da abokin aiki Ibrahim Ahmed yayi da wakilinmu dake Abuja an samu tabbacin cewa shugabankasar Najeriya ya kori duk shugabannin sojojin kasar tare da mai bashi shawara akan harkokin tsaro ya kuma nada wasu sabbi.

Bayan da shugaban ya gana da hafsoshin ya sallamesu. Nan gaba za'a bayyana dalilin saukar dasu.

Amma kafin nan ga sunayen sabbin hafsoshin da shugaba Buhari ya nada:

1. Manjo Janar Abayomi Gabriel Olonishakin shi ne hafsan hafsoshi. Dan asalin jihar Ekiti ne

2. Manjo Janar T.Y. Buratai shi ne hafsan sojojin kasa daga jihar Borno

3. Rear Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas shi ne hafsan sojojin mayakan ruwa daga jihar Cross Rivers

4. Air Vice Marshal Sadique Abubakar shi ne hafsan sojojin mayakan sama dan asalin jihar Bauchi

5. Air Vice Marshal Monday Riku Morgan shi ne hafsan dakarun leken asiri daga jihar Benue

6.Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya) daga jihar Borno shi ne mai ba shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG