Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ka Iya Daidaita Alamuran Najeriya-inji Amurka


Mr. Tony Blinken mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka
Mr. Tony Blinken mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka

Mukaddashin sakataren harkokin wajen Amurka Tony Blinken yayi taron manema labarai a ofishin jakadancin Amurka dake Abuja.

Mr Tony Blinken yace Shugaba Muhammad Buhari ka iya daidaita alamura a Najeriya kuma Amurka zata duba yadda zata kawo dauki.

Yace a ganawar da yayi da shugaba Muhammad Buhari sun tattauna hanyoyin da za'a bi domin inganta tsarin tsaro musamman ganin yadda kungiyar Boko Haram ke kara yiwa kasar barazana.

Amurka zata kuma tallafawa tattalin arzikin kasar. Zata taimaka wurin yakar cin hanci da rashawa kana a kuma tabbatar da gwamnati ta saukar da nauyin dake kanta kamar yadda ya kamata.

Mr. Tony Blinken yace Amurka na yin Allah wadai da yadda Boko Haram ke cigaba da kai hare hare a masallatai da kuma mijami'u.

Domin kawo karshen kungiyar Boko Haram Mr. Blinken yace akwai bukatar samun kyakyawan shugabanci nagari da adalci tsakanin 'yan kasa da mutunta hakin bil Adama da tabbatar da tsaron dan kasa da tsaro mai dorewa a wuraren da aka kwato daga hannun Boko Haram a arewa maso gabashin kasar.

Mukaddashin sakataren harkokin wajen Amurkan yace yadda huldar diflomasiya zata kasance tsakanin kasashen biyu shi ne me Amurka zata cimma Najeriya ba me Amurka zata yiwa Najeriya ba.

Yace Amurka zata kawo tallafi wajen ganin an kubutar da 'yan matan Chibok da ma sauran 'yan Najeriya da Boko Haram ke garkuwa dasu. Amurka zata marawa Najeriya wajen horas da jami'an tsaro da samar masu da kayan aiki irin na zamani da musayar bayanan sirri.

Yace cin hanci ba karamin illa ba ne saboda haka yace tuni kasarsa ta yi nisa wajen tallafawa EFCC da kayan aiki irin na zamani da ma horas da jami'anta. Bugu da kari ya ce Amurka zata taka rawar gani wajen gano kudaden haram da aka sace aka kuma boyesu a kasashen ketare.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina.

Shugaba Muhammad Buhari Ka Iya Daidaita Alamuran Najeriya-inji Amurka - 2'05"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:05 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG