Gwamnatin Najeriya, ta hannun hukumar kula da shaidar zama dan kasa ta kasar (Nimc), ta jaddada aniyar kaddamar da katin zama dan kasar da aka inganta, wanda zai zamo katin komai da ruwanka, nan ba da jimawa ba a shekarar da muke ciki.
Sanarwar da NIMC ta fitar ta bayyana sabon katin shaidar dan kasa da falle daya, mai saukin amfani kuma na komai da ruwanka (GMPC), da zai kawar da bukatar katuna da dama.
NIMC ta wallafa cewa “kamfanin Afrigo ne zai gudanar da sabon katin da aka kirkira da hadin gwiwar babban bankin Najeriya (CBN) da hukumar daidaita hada-hada tsakanin bankuna (NIBSS), a matsayin wani tsarin amfani da katin a Najeriya da CBN ya sahale domin samar da hada-hadar biyan kudi ta kati mai araha kuma budaddiya.”
A halin yanzu, akwai bankunan kasuwanci da kananan bankunan bada lamuni 26 da ke bayar da katunan Afrigo a fadin kasar.
A cewar NIMC, fasahar za ta magance bukatar tantancewa ta zahiri tare da baiwa masu amfani da kati domin fayyace bayanai da cin gajiyar ayyukan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu.
Game da batun katin zabe, hukumar tace tana gudanar da tarurruka da hukumar zabe ta kasa (INEC) na
Dandalin Mu Tattauna