An kubutar da mata masu juna 2 guda 9 daga wani wurin kyankyasar jarirai a Abuja, babban birnin najeriya.
Jami’an hukumar NAPTIP, mai yaki da fataucin mutane a Najeriya ne suka kubutar da matan, kamar yadda hukumar ta bayyana a yau Alhamis.
A sanarwar daya fitar, kakakin hukumar NAPTIP, Vincent Adekoye, yace makyankyasar jariran na nan a rukunin gidaje dake yankin Ushafa na birnin tarayyar Najeriya.
A cewar Adekoye, sun kai samame akan wurin ne bayan samun bayanan sirri daga wani dan kasa na gari.
“Wani mai fataucin mutane da ba’a tantance ko wanene ba ne ya kulle matan ne a cikin wani gidan haya dake rukunin gidajen bayan daya daukesu aiki ta hanyar amfani da wani dandalin yanar gizo,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.
A wani labarin kuma, NAPTIP ta samu nasarar gurfanarwa tare zartar da hukunci akan wani limamin Kirista a Abuja wanda ya yiwa ‘yar wani mamba a cocinsa fyade a watan Maris din 2023.
A cewar NAPTIP, wata kotun tarayya dake zamanta a Gudu, karkashin jagorancin Mai Shari’a Adebiyi Osolo ta yankewa limamin da aka samu da laifin fyaden hukuncin zaman kurkuku na shekaru 20 ba tare da zabin tara ba.
Limamin mai shekaru 52 da aka bayyana sunansa da Kenneth Duke shine ya assasa shahararren cocin dake kan babban titin Dantata zuwa Zuba.
Dandalin Mu Tattauna