Mai Shari’a James Omotosho na babbar kotun tarayya dake Abuja ya haramta kungiyar Lakurawa, inda ya bayyanata da ta ‘yan ta’adda.
Umarnin haramtawar ya biyo bayan bukatar hakan da antoni janar na tarayya kuma ministan shari’ar Najeriya, Lateef Fagbemi, ya gabatar.
A hukuncin daya zartar, Mai Shari’a Omotosho, ya kuma haramta kungiyoyin irinta da ke gudanar da harkokinsu a Najeriya, musamman yankunan arewa maso yamma da arewa maso tsakiyar kasar.
“Don haka na zartar da umarni kamar haka: cewar an ba da umarnin da ya ayyana ayyukan kungiyar lakurawa da sauran kungiyoyi irinta a kowane yanki na najeriya, musamman a arewa maso yamma da arewa maso tsakiyar Najeriya a matsayin ayyukan ta’addanci kuma haramtattu.
“Don haka an bada umarnin da ke haramta kasantuwar Lakurawa da sauran kungiyoyi irinta a kowane yanki na Najeriya, musamman a arewa maso yamma da arewa maso tsakiyar Najeriya a kungiyance ko a daidaiku a kowane irin suna zasa kira kansu tare da wallafa hakan a jaridar hukuma da sauran jaridun kasar guda 2.
Dandalin Mu Tattauna