Daga yanzu Kenya za ta kyale kusan dukkanin ‘yan Afrika su ziyarci kasarta ba tare da neman iznin yin hakan ba, a matsayin sabon umarni daga majalisar zartarwar kasar
Sanarwar da majalisar zartarwar ta fitar ta fayyace cewar za’a soke bukatar neman iznin tafiye-tafiye ga ilahirin ‘yan Afrika, in banda ‘yan kasashen Somaliya da Libya, saboda dalilai na tsaro.
A karkashin tsarin da aka yiwa kwaskwarima, za’a kyale galibin ‘yan Afrika su shiga Kenya kyauta ba tare da neman izini ba tsawon watanni 2.
Buga da kari, za’a kyale mambobin kungiyar kasashen gabashin Afrika-da suka hada da Uganda, Tanzaniya, Rwanda da Burundi-su zauna a kasar tsawon watanni 6 a bisa dacewa da manufar kungiyar.
Dandalin Mu Tattauna