Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya (NAFDAC) ta lalata kayayyakin jabu da wadanda wa’adin amfani dasu ya kare da kuma marasa inganci na kudi Naira bilyan 1.3 a Abuja.
Babbar daraktar NAFDAC, Farfesa Moji Adeyeye, wacce ta samu wakilcin Festus Ukadike, wanda ya jagoranci jami’an hukumar zuwa wurin zubda shara na Kuje dake Abuja, yace kayayyakin da aka lalata din sun hada da magunguna da kayan aikin asibiti da kayan kwalliya dana abinci da sauran kayayyaki da dama.
Haka kuma nafdac ta lalata kayan abincin da wa’adin amfani dasu ya kare da wasu kungiyoyin Najeriya dama na kasa da kasa suka mika mata bisa radin kansu, ciki harda hukumar abinci ta duniya (WFP).
Dandalin Mu Tattauna