Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Sanda Sun Ceto Matar Mataimakin Babban Sufetonsu Mai Ritaya


'Yan sandan kwantar da tarzoma a Najeriya
'Yan sandan kwantar da tarzoma a Najeriya

Kwamishinan ‘yan sanda jihar Ogun, Lanre Ogunlowo, ne ya jagoranci aikin daya kai ga kubutar da matar aig odumosu mai ritaya.

Jami’an ‘yan sandan Najeriya sun yi nasarar kubutar da Folashade Odumosu, matar wani tsohon mataimakin babban sufetonsu, Hakeem Odumosu daga hannun masu garkuwa da mutane.

Matar ta kubuta ne a jiya Laraba.

An bayyana cewar kwamishinan ‘yan sanda jihar Ogun, Lanre Ogunlowo, ne ya jagoranci aikin daya kai ga kubutar da matar aig odumosu mai ritaya.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya, Muyiwa Adejobi, ne ya bayyanawa tashar talabijin ta Channels hakan yayin wata hira ta wayar tarho a yau Alhamis.

Yayin samamen, an hallaka masu garkuwa da mutanen.

Adejobi ya kara da cewar, jami’ansu sun kuma kwato kudin fansar da aka biya masu garkuwar a matsayin tarko.

Sai dai, yaki ya bayyana adadin kudin da aka biya masu garkuwar ko wurin da aka kubutar da matar.

Adejobi ya ci gaba da cewarbabban sufeton ‘yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya yabawa kwamishinan da jami’ansa akan kokarin kubutar da matar.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG