Idi Barau mai magana da yawun ofishin jakadancin Amurka dake Niamey ya bayyana abun da kasar ta Nijar zata yi da tallafin dalar Amurka miliyan uku da zata samu.
Yace za'a yi anfani da kudaden ne wajen yaki da ayyukan ta'adanci. Kudin zai kuma tallafawa ma'aikatar shari'a wajen kawo sauy-sauye cikin dokokin kasar da suka shafi ta'adanci da kuma gudanar da gidajen wakafi. Za'a gyara gidajen kurkuku da nufin ingantasu tare da gyara ofisoshin ma'aikatar shari'a.
Wani kaso na kudin za'a yi anfani dashi wajen samar ma ma'aikatar shari'a ingantattun kayan aiki.
A cikin jawabinta karamar ministar harkokin wajen Nijar Madam Kafa Kistan Jaku ta bayyana irin tasirin da tallafin zai yi a fannonin da aka lissafa. Tace yarjejeniyar ta tabo fannin tsaro da kuma gudanar da ayyukan fannonin shari'a. Fannonin su ne gwamnatin Nijar ta fi mayar da hankali a kai. Tana yaki da ta'adanci da kuma kawar da gallazawa mutane tare da rage cunkoson da ake fama dashi a gidajen kaso.
Wannan yarjejeniyar ita ce ta biyu cikin tallafin da kasar Amurka take ba Nijar wadda ta zo daidai lokacin da kasar ke yakar kungiyar Boko Haram tare da hadin kan wasu kasashen yammacin Afirka.
Ga rahoton Yusuf Abdullahi.