Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Burkina Faso Sun Farma Takwarorinsu da Suka Yi Juyin Mulki Makon Jiya


Janar Gilbert Diendere shugaban juyin mulkin da bai dore ba saboda matsin shugabannin kasashen yammacin Afirka
Janar Gilbert Diendere shugaban juyin mulkin da bai dore ba saboda matsin shugabannin kasashen yammacin Afirka

Sojojin Burkina Faso sun kara da sojojin da suka yi juyin mulki makon jiya amma kawo yanzu ba'a san adadin wadanda suka rasa rayukansu ba.

Madugun juyin mulkin da bai yi nasara ba a Burkina Faso, Janar Gilbert Diendere, yana fargabar "mutane da dama sun mutu", bayan da sojojin kasar suka kai farmaki kan wani sansani da bijirarrun sojojin da suke kare fadar shugaban kasar, wadanda suka ki a jiye makamansu.

Janar Gilbert wanda yayi magana da kamfanin dillancin labarai na Faransa daga wani wuri da ba’abayyana ba a daren jiya Talata, bayan farmakin da sojojin kasar suka kai kan inda suke. Yace akwai iyalai da wurin shan magani, a sansanin da yake Ouagadougou, babban birnin kasar.

Diendere ya yi magana ta Radio tun farko a jiya, inda yayi kira ga sojojin da suka bijire su ajiye makamansu. Rundunar sojojin kasar tace kimanin sojoji 300 cikin 1,300 da suka yi juyin mulkin ne suka yi saranda.

Rahotannin farko da aka samu, sojojin sun shiga sansanin ba tareda wata turjiya ba, sai dai babu cikakken bayanin abunda ya faru da ya kai ga bude wuta.

Sojojin da suke gadin fadar shugaban kasar, sun amince zasu ajiye makamansu a yarjejeniyar da aka cimma makon jiya, wanda ya kawo karshen juyin mulkin da baiyi karko ba. Sojojin sun nemi tabbacin babu abunda zai taba lafiyarsu data iyalansu.

Janar Diendere, da sojojin da suke karkashinsa sun ayyana juyin mulkin ne ranar 16 ga watan nan, domin rashin jin dadinsu gwamnatin wucin gadin kasar ta hana magoya bayan tsohon shugaban kasar Blaise Compaore shiga takarar zaben kasar da ake shirin yi.

XS
SM
MD
LG