Tuntubar junan inji kakakin ma'aikatar Peter Cook, shine tabbatar da cewa matakan da runduar taron dangin take dauka a Sham, bai fuskanci wani tsaiko ba, daga abunda Rasha take yi a kasar.
Cook, yace Rasha da rundunar taron dangin, zasu maida hankali "wajen kaucewa rigima tsakaninsu", ko rage hadari a sararin samaniya, ta wajen gayawa juna inda jiragen samansu suke.
Jami'an ma'aikatar tsaron Amurkan sun bada labarin cewa Rasha ta tura jiragen yaki da kuma dakarunta zuwa Syria cikin 'yan makonnin baya bayan.
Ranar Litinin ne shugabannin kasashen biyu na Amurka Barack Obama daVladimir Putin na Rasha, suka gana a gefen taron Majalisar Dinkin Duniya a New York, domin fara shawarwari ta fuskar soji, gameda matakai na zahiri da abun da zasu yi a Syria.