Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mazauna Yankin Madagali Sun Soma Gudu Zuwa Yola


Masu arcewa daga yankin Madagali
Masu arcewa daga yankin Madagali

Kwanaki hudu bayan da 'yan Boko Haram suka kai hari a Bakin Dutse kusa da Gulak cikin karamar hukumar Madagali jihar Adamawa mazauna yankin na arcewa zuwa Yola.

Wannan sabon gudun hijiran na zuwa ne bayan watanni goma sha daya da komawar mutanen gida daga gudun hijiran farko da suka yi.

Malam Abdulkarim Sayid daya daga cikin wadanda suka yi hijira zuwa Yola ya ce hankulan jama'ar karamar hukumar Madagali ya tashi saboda suna zama cikin fargaba. Yankin nasu dai yana kurkusa da dajin Sambisa inda yan Boko Haram suka kafa sansanoninsu.

Mutanen yankin sun zargi gwamnatin jihar Adamawa da rashin kulawa da kuma rashin kai dokin gaggawa. Amma gwamnatin jihar ta kare kanta ta bakin kakakin gwamnatin jihar Yohana Mathias.Yace gwamnati ta aika da jami'an tsaro domin kare jama'a.

Wani da 'yan ta'adan suka kone gidansa yace zai yi wuya yanzu su koma yankinsu. Bayan ya gudu daga garinsu sai kuma ya hadu da sojoji da suka lakada masa kashi.

Mai wakiltar Madagali a tarayyar Najeriya Adamu Kamale ya tabbatar da cewa jama'ar yankinsa suna tururuwa zuwa Yola. Yace basu da zabi illa su koma sansanonin 'yan gudun hijira ko kuma gidajen dangi da 'yanuwa.

Ga rahoton Sanusi Adamu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG