Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muddin Koriya Ta Arewa Ta Amince, Amurka Na Shirye Ta Hau Teburin Shawarwari Da Ita


Tillerson ya ce zamu cigaba da neman hanyar da za mu tattauna, amma wannan ya rage ga shugaba Kim.

Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya fadi cewa a shirye Amurka take ta hau teburin shawarwari da Koriya ta Arewa, yayinda Kim Jong Un ya dage barazanar da yayi ta harba makamai masu linzame a yanken Guam na Amurka dake gabar tekun Pacific.

Yayinda akwai bukatar yin amfani da hanyar diplomasiyya, Amurka ta ce dole ne Koriya ta arewa ta daina gwajin makamai masu linzami da na nukiliya kafin ma a fara tattaunawar akan yadda za a kawarda makaman nukiliya a mashigen koriyoyin biyu.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka Heather Nauert, ta fada jiya Talata cewa “za mu tattauna da Kim Jong Un, a lokacin da ya dace. “Idan Koriyar ta nuna alamun tana da ra’ayin kokarin da ake yi na kawarda da shirin makaman Nukiliya a yankin.

Kwararru sun ce gwajin makami mai linzamen da Koriya ta arewa tayi ranar 4 ga watan Yulin da kuma ranar 28 ga watan na Yulin da ya gabata, ya nuna cewa kasar zata iya farwa yankin Alaska da ma ciki-cikin Amurka sosai.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG