Kamar yadda muka saba a kowane karshen mako, dandalin voa yana kawo maku shirin samartaka, inda zaku ji ra'ayoyin matasa maza da mata a game da halaiya da zamantakewar yau da kulum kamar yadda zamani ke tafiya.
A wannan makon, mun sami zantawa ne akan illolin da wayar hannu ke yi ga samari da 'yan mata da kuma al'umma musamman saboda yadda samarin kan raba dare suna chatting kokuma waya tsakanin su da abokai ko 'yan mata.
Kamar yadda mafi rinjaye daga cikin samarin suka bayyana, sukan yi amfani da wata dama ce da kamfanonin wayar ya basu musamman na samun lokacin da zasu zanta da abokan huldar su a kyauta ba tare da sun sa katin waya ba. koda shike da dama sun bayyana cewa iyayensu sun hana su, wasu da dama kuma sun ce iyayen ma basu san cewar suna yin wayar ba domin kuwa ba gida guda suke kwana ba.
Da muka karkata daya bangaren kuma, wasu daga cikin matasan sun ce koda iyayen na daki daya dasu, babu yadda zasu san cewa suna magana domin basa daga murya, kuma sun nuna cewar akwai batutuwa da dama da suke tattaunawa akai wadanda wasu basu da ma'ana, wato sukan yi maganganun batsa domin basa ganin fuskokin juna.
Wannan ba karamar matsala bace domin kuwa rashin isashshen barci, da fada ma juna maganganun da basu dace ba duk bashi chikin tarbiyar da yakamata matasa su tashi da ita.
Dan hakane muka gaiyaci malami a fannin zamantakewa da halayyar dan adam daga jami'ar Bayero dake Kano domin yi mana fashin baki akan yadda wannan zai shafi halayyar dan' adam da kuma al'umma da kanta. ku biyo mu domin jin yadda ta kaya.
Ku saurari cikkaken shirin a dandalinvoa,com