Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa matsalar tsaro da kungiyar Boko Haram ta haddasa ya durkushe ilimi a arewa. Dama can kudancin kasar ya tserewa arewa a ilimin boko amma kuma sai gashi Boko Haram ta kara dagula ilimi a arewa. Hare -haren da kungiyar ke kaiwa makarantu sun karyawa iyayen yara karfin gwiwar aika 'ya'yansu makarantu. 'Yan Bok Haram suna kai hari koina suka ga dama kuma a kowane lokaci ba tare da yin la'akari da birni ko kauye ba. Yanzu kam babu wata makaranta a yankin arewa da ta tsira.
A cikin binciken da aka gudanar a cikin kowane yara dari da ashirin na jihar Borno yara ashirin da tara ne kawai ke karatun boko sabanin abun dake faruwa a jihar Anambra inda a cikin yara dari da shirin yara dari da goma ne ke karatun boko. A jihar Zamfara cikin yara dari da ashirin yara ashirin da takwas ne ke karatun boko sabanin abun dake faruwa a jihar Ondo inda cikin yara dari da ashirin yara dari da goma shatara ne ke karatu.
Idan aka leka jihar Kebbi yara talatin da takwas ke karatun boko a cikin yara dari da ashirin amma a jihar Cross Rivers yara dari da goma sha hudu ne ke karatu cikin dari da ashirin. Idan an cigaba da binciken haka lamarin yake tsakanin jihohin arewa da na kudu.
Matsalar tsaro dake da nasaba da ilimin boko ya ddabi yankin arewacin Najeriya.
Dr Bawa Abdullahi Wase ya bada mafita yadda arewa zata farfado daga tabarbarewa ilimin da ta samu kanta. Yace wani abun dake faruwa shi ne yadda ake anfani da 'yan sanda su tsare gidajen giya. Babu inda ake haka a kowace kasa a duniya. Idan ana son a kawar da matsalar tsaro domin a inganta ilimi a baza 'yansanda da sojojin dake cikin bariki zuwa makarantu su karesu. A kara daukar ma'aikatan tsaro a kuma basu kayan aiki na zamani. Idan an yi hakan zai taimaka. Matasa kuma da suke nan basu da aiki gwamnati ta nema masu abun yi.
Tsohon kwamishanan 'yansandan jihar Legas Abubakar Tsav ya bada shawara a kewaye kowace makaranta da katanga.
Ga rahoton Ladan Ibrahim Ayawa.