'Yansandan da aka kama sun amsa tuhumar da rundunar sojan da ta kamasu take yi masu. Dama aikin da su keyi kenan na sayar da makamai wa 'yan tada kayar baya a rewa maso gabas.
Mutanen sun taso ne daga birnin Owerri. Cikin makaman da suke dauke dasu sun hada da AK 47 guda 40 da magazin-magazin da dama. Akwai kuma akwatuna guda hudu makare da harsashen AK 47 da dai sauransu.
Rundunar sojojin Nsukka tace tana rike da mutane hudu kuma da zara ta kammala bincike zata mika mutanen ga 'yansanda. Ita ma rundunar 'yansandan jihar Enugu tace ta ji wani labari kamar hakan amma tana dakon isowar batun gabanta.
'Yan arewa da suka dade suna zaune a yankin kudu maso gabashin kasar kamar Abubakar Lemi yayi tsokaci dangane da matsalar. Yace lamarin yana da matukar tashin hankali da ban tsoro domin suna zama lafiya a yankin ba tare da wani tashin hankali ba amma yau sai gashi wanda za'a kai kara gareshi shi ne kuma ake zargi da sarafa miyagun makamai. Yana fata idan sojoji sun kammala bincike su mika mutanen ga wadanda zasu hukuntasu daidai da laifin da suka yi.
Dr Aminu Maude na Jami'ar Usmanu Dan Fodio dake Sokoto yace idan gwamnati na son magance tabarbarewar tsaro a fuskanci matsalar ba sani ba sabo. Kowa yayi a yi masa. Kada a yi anfani da bangaranci ko addini ko kabilanci ko siyasa. Duk wanda aka ga yana da hannu a ciki a dauki matakan da suka kamata a kansa.
Ga rahoton Lamido Abubakar Sokoto.