Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsalar Aikin Yi, Ina Mafita?


Matasa Yaro Mai Sayar da Awara
Matasa Yaro Mai Sayar da Awara

A yayin da talauci da rashin aikin yi ya dabaibaye matasa a Najeriya, Dr Tukur Mohammed Baba, malami a fannin zamantakewar al’uma a jami;ar Usman Danfodiyo da ke jahar Sokoton Najeriya, yayi Karin bayani akan matsalolin da ke haifar da wadannan matsaloli.

A cewar sa, sha'anin rashin aikin yi matsala ce wadda ta fara zama abin bantsoro domin kuwa idan ka duba zakai ta ganin gungu gungu na matasa a unguwanni daban daban kuma ba abin da suke yi sai zaman kashe wando.

Al'amuran kara lalacewa su ke kullum musamman ganin yadda matashi zai kammala karatun jami'a amma karshenta sai dai ya koma karkashin iyayen sa sa'an nan ya sami abin da zai sa a baki. idan akayi la'akari da yadda rayuwar take da farko, gwamnati ke daukar yawancin dawainiyar matashin da ya gama karatu wajan samar masu aiki da sauran su.

kadan daga cikin abubuwan da suka kara kaimin matsalolin sun hada da Gwamnati da kuma tsari namu na mulki, ba lallai na gwamnati ba hatta na gargajiya ma ya tabarbare ba kamar yadda ya kamata ya kasance ba domin kuwa gwamnati ta cire hannunta wajan taimakawa matasa.

Akwai kuma matsalar cin hanci da rashawa wanda ko aiki matashi ya je nema sai ya bada cin hanci kafin a dauke shi aiki. daga karshe kuma akwai matsalar da jama'a suka dorawa kansu ta shagwaba wato dole sai aikin gwamnati.

Ga karin bayani.

XS
SM
MD
LG