Allurar riga kafi muhimiyar abuce, a wannan karo a kokarin kara wayar da kan al’uma a kan mahimancin bama yara allurer riga kafi, ya sha banban da na saurna lokutta. A wannan karon an fito da wani sabon salon yawo gida gida don diga wannan magani ga yara ‘yan kasa da shekaru biyar, wanda ake tafe da yara wadannada suka kamu da wannan jarabawar ta shan’inna don nuna ma iyaye yadda take nakasa yara.
A zantawa da wakiliyar DandalinVOA tayi Baraka Bashir, ta zanta da Malama Amina Abdullahi, wadda take daya daga cikin wadanda suka kamu da wannan cuta ta rashin ginannen jiki. Ita dai Amina, tana kira ga iyaye da su bada ‘yayansu a basu wannan allura don kuwa idan ba’a yimusu wannan allurer ba suna iya kamuwa da wannan cuta wadda ke tauyar da yara maza ko mata.
Ta yi nuni da cewar idan yaro ya kamu da wannan cutar to lallai wannan yaro bazai iya wasu ayyuka a rayuwar sa ba, hasalima yasamu nakasa a rayuwa don kuwa idan akayi la’akari da yawan masu nakasa za’a ga cewar bakomai suke iyayi a rayuwa ba, musaman ma yanzu idan akayi la’akari da yawan kanana hukumomi 44 da ake dasu a jihar Kano, za’aga cewar ba a tabayin Kansila ko Ciyaman nakasashe ba. Idan kuma aka koma ta bangaren mata to za’a ga cewar idan yarin ya tana da nakasa to zaiyi wuya asamu mai aurenta. To a zahirin gaskia dolle ne iyaye su bada ‘yayansu don a kawar da su daga irin wannan hali da sukan iya fada mawa.