An yi wani arangama tsakanin Nufawa da Fulani makiyaya a yankin Pategi dake cikin jihar Kwara a Najerya, inda Kimanin Fulani makiyaya ashirin suka rasa rayukansu.kashe tare da kona gawarwakinsu a yankin Pategi dake jihar Kwaran Najeriya sanadiyar wani hari da aka kai masu.
Shugaban kungiyar Fulani ta Miyetti Allah reshen jihar Kwara, Alhaji Usman Adamu ya shaidawa wakilin Muryar Amurka, Mustapha Nasiru Batsari, cewa harta gidajensu da wasu kaddarorinsu dama wasu gawarwaki aka kona sakamakon harin.
Yace an dauki mako guda ana kai masu hari jefi-jefi. Ya kara da cewa har yanzu lamarin bai tsaya ba. Yace an kashe yara da mata da tsoffi ba tare da wani dalili ba.
Kungiyar Miyetti Allah ta Najeriya tace ta samu labarin tashin hankalin kuma tana daukan mataki kamar yadda mataimakin shugaban kungiyar na kasa Alhaji Hussaini Boso ya sanar. Yace zasu rubutawa gwamnan jihar da sarkin Pategi, Yace yana ganin ba daidai ba ne a kebe wata kabila a ce za'a kawar da ita daga doron kasar duniya.
Amma sakataren masarautar Pategi Alhaji Muhammad Ibrahim yace lamari ne na shaidan kuma kawo yanzu an shawo kan matsalar. Yace kwamishanan 'yan sanda Alhaji Salihu Garba ya aiko an zauna an daidaita da juna.Yace an kira bangarorin biyu an tattauna. Yanzu kome ya lafa.
Wakilin Muryar Amurka Mustapha Batsari, yayi kokarin samun kwamishinan yan sandan jihar Kwara Alhaji Salihu Garba, amma abin ya ci tura har ya aika masa sakon kata gwana duk ba'a yi nasara ba.