Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abubuwan da Suke Yin na Hadin Kai


Gwamnan jihar Pilato Simon Lalon yace ya yanzu sun bankado cewa gwamnatin data shude na Jonah Jang ta bar musu bashin Naira miliyan dubu 104.

A tattaunawar da gwamnan yayi da wakiliyar Muryar Amurka Zainab Babaji, yace gwamnatin za ta nada kwamiti da zai bi diddigin basussukan da gwamna Jonah Jang ya bari da kuma matakan da sabuwar gwamnati zata dauka.

‘’Ta bar mana bashin Miliyoyi ba a gama tantance basussukan ba tukuna ana zaton idan aka gama zai karu kuma abinda ya bani mamaki shine abinda za'a bar gwamnatin da zata shiga wato namu gwamnatin shine miliyan 90, miliyan 90 bai ma isa ya biya ma'aikata guda daya ba a jihar Filato, kuma muna bukatar bilayan ne da yawa wanda zamu biya ma'aikata to abinda na gani ya kawo muna damuwa ke nan dole ne a duba domin kudi na jama'a ne ba za'a bar kudi su tafi haka ba, yanzu munsa a bido muna ainihin basussukan da aka bari da kuma ainihin kudaden da yakamata a bari, dole mun fuskanci abinda zamu yi ayi gyara sabo da gobe.

Ba wai ana neman ayi fada bane ko ace ana fada da wanda ya bar gwamnati bane a’a, domin kayan gwamnati kayan jama'a ne dole ne mu lura dashi, mu duba inda kudade suka fita inda kudade suka bata domin a dawo dasu domin mu samu gyara, ba zamu waiwayi baya ba’’

Gwamnan ya kara da cewa abbuwan da suke yin na hadin kai ne sun hada da tabbatar da ganin cewa an shigar da kowace kabila a wannan gwamnati idan ba wani abu ba da ikon ALLAH zamu bi duk hanyoyi da kowa zaiji dadi ya samu jin dadin zaman lafiya a Filato’’.

Sai wakiliyar sashen Hausa Zainab Babaji ta kasa samun wanda zai mayar da martini daga bangaren tsohon gwamnan.

XS
SM
MD
LG