Kungiyar IZALA ta kaddamar da Rediyo da Talibijan akan tauraron dan-Adam mai suna MANARA.
Kaddamarwar ta zo daidai lokacin da Najeriya ke harsashen cewa duk kafafen rediyo da talibijan na kasar su koma kan tauraron dan-Adam daga na gargajiya da aka saba, cikin wannan watan.
Kafin kaddamar da Manara, tuni wasu gidajen Rediyo da Talibijan masu zaman kansu suka koma kan tauraron dan-Adam din.
Kamar Manara yawancin gidajen Rediyo da Talibijan na Hausa dake kan tauraron dan-Adam suna watsa shirye-shiryensu ne daga waje saboda tsaurin dokokin Najeriya na bada lasisin kafasu.
Tashar Manarar da yanzu take yada wa'azin addinin Musulunci da wayar da kawunan alhazai kusan su dubu dari da hira kan tattalin arziki da hadin kan al'umma na aiki ne kan tauraron NAISAT.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da kafar MANARA, Gwamna Abdulaziz Yari Abubakar na jihar Zamfara, Yace musulunci ya samu nasara ne tare da yin wa'azi. Idan bada wa'azi ba da ba'a samu yaduwar addinin ba.
Shi ma Sultan Abubakar ya bukaci tashar ta fadada ayukanta da yin anfani da harshen turanci domin sako ya samu kabilu a saukake.
Shugaban IZALA Sheikh Abdullahi Bala Lau yace tashar zata hada da ni shadantarwa mai ma'ana ta zama kafar yada wa'azi ga miliyoyin mutane a saukake. Yace basu soma karanta labarai ba amma zasu hada shi da shiri domin mata da tattalin arziki da dai sauransu.