Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Tuhumar Wasu Mutane 26 Da Ake Zargi Da Satar Danyen Mai


Wata kotu a Najeriya ta tuhumi wasu mutane 26 da laifin hada baki wajen aikata laifin kanruwa da kuma yunkurin yin cinikin danyen mai ba bisa ka'ida ba, bayan da hukumomi suka zargi jirginsu da shiga sararin ruwan Najeriya ba tare da izini ba.

Kyaftin din dan kasar Indiya ne yayin da ma'aikatan jirgin suka fito daga Poland, Indiya, Sri Lanka da Pakistan, kamar yadda takardun kotu suka nuna.

Kotu
Kotu

Bisa bukatar hukumomin Najeriya, kasar Equatorial Guinea ta tsare jirgin mai suna Heroic Idun, mai dauke da ganga miliyan 2 na mai a ranar 17 ga watan Agusta, bisa laifin tafiya ba tare da wata tuta ba, ya kuma tsere daga hannun sojojin ruwan Najeriya, ya yi tafiya a cikin ruwan Equatorial Guinea ba tare da izini ba.

Mutanen 26 da suka hada da kyaftin din, sun gurfana a wata babbar kotu da ke birnin Fatakwal na jihar Rivers a ranakun Litinin da Talatan nan, inda alkalin kotun ya bada umarnin a tsare su a cikin jirginsu karkashin gadin sojojin ruwan Najeriya.

Mutanen, wadanda dukkansu suka musanta tuhumar, ana zarginsu da "kokarin satar danyen man fetur a yankin Najeriya ba tare da izini ba."

Najeriya dai ta ce jirgin bai riga ya yi lodin mai ba kafin sojojin ruwa su tunkaro shi, sai dai ya shiga wani yanki da aka takaita ba tare da izini ba sannan ya yi yunkurin lodin danyen mai ba bisa ka'ida ba.

Kamfanin man fetur na kasar ya bayyana cewa, satar mai ya kai sama da ganga 400,000 a kowace rana daga man da Najeriya ke hakowa, ya kuma durkusar da kudaden kasar, ya maida kasar dake kan gaba a hakar mai a nahiyar Afirka zuwa ta biyu.

-Reuters

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG