Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mun Gano Wata Hanya Da Ake Sace Man Fetur Din Najeriya Ta Teku - Mele Kyari


Mele Kyari
Mele Kyari

Jami'ai a Najeriya sun gano wata hanyar da ba ta dace ba daga daya daga cikin manyan tashoshinta na fitar da mai zuwa cikin teku wanda ya shafe shekaru tara ba a gano shi ba, in ji shugaban kamfanin mai na kasar NNPC LTD.

WASHINGTON, D.C. - An gano hanyar satar mai tsawon kilomita 4 (mil 2.5) daga tashar jiragen ruwa na Forcados, wanda yawanci ana fitar da kusan ganga 250,000 a kowace rana (bpd) na mai zuwa cikin tekun a yayin da ake dakile sata a cikin makonni shida da suka gabata, Shugaban NNPC, Mele Kyari ya fadawa kwamitin majalisar da yammacin ranar Talata.

Hedikwatar NNPC
Hedikwatar NNPC

"An kwashe sama da shekaru 22 ana satar man fetur a kasar amma yawan wanda aka kwasa a 'yan kwanakin nan ba a taba ganin irinsa ba," in ji Kyari a wani faifan murya na bayanai da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya sake dubawa.

Barayi sau da yawa suna fasa bututun da ke kan ƙasa don kwashe mai ba tare da an gano shi ba yayin da suke ci gaba da aiki.

Kamfanin Forcados SPDC, wani reshen Shell SHEL.L, ya ce bututun satar ya yi nisa.

Kamfanin mai na Shell
Kamfanin mai na Shell

“SPDC ta yaba da karin sa ido da aka yi a madadin kamfanin na NNPC don magance ta’addanci,” kamar yadda kakakin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters ta email.

"Duk da haka, bututun satar da aka gano kwanan nan yana da nisan kilomita 30 daga tashar Forcados ta SPDC. Ba ya cikin bututun SPDC."

Kyari ya ce Najeriya, wadda ita ce kasar da ta fi kowace kasa fitar da mai a Afirka, tana asarar kudaden shiga daga kusan bpd 600,000 na man fetur, in ji Kyari.

Fitar da danyen mai ya fadi kasa da bpd miliyan 1 a cikin watan Agusta a karon farko tun akalla 1990.

An dakatar da lodin kaya a tashar tun bayan da aka gano wata hanya mai daga wani bututun ruwa a tashar a ranar 17 ga watan Yuli.

Shell ya ce a wannan makon yana sa ran za a ci gaba da lodin a cikin zango na biyu na watan Oktoba.

A watan Agusta, kamfanin NNPC ya bai wa kamfanoni da suka hada da na tsoffin tsagerun kwangilolin yaki da satar mai.

-Reuters

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG