ABUJA, NIGERIA - A daidai lokacin da ‘yan Najeriya da suka hada da ‘yan kasuwa, direbobin fasinjoji, masu ababen hawa, masu kanana da matsakaitan sana’o’i ke ci gaba da kokawa a game da matsalar karancin mai da dogayen layi da suke fuskanta idan suka je neman mai don su gudanar da al’amurran su na yau da kullum, kungiyar mamallakn motocin mai ta NARTO da takwararta kungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu wato IPMAN sun tabbatarwa ‘yan kasar cewa, nan da mako guda za a kawo karshen wahałar mai da ake gani a manyan biranın Najeriya.
Tuni dai ’yan bunburutu suka fara amfani da wannan matsalar wajen cin nasu kasuwa inda suke sayar da litar man fetur a kan Naira 240 zuwa 400 a yawancin sassan kasar nan da suka hada da manyan birane kamar su Abuja, Legas, Fatakwal da dai sauransu.
Shin akwai mafita ga wannan al’amarin karancin man fetur da ya ki ci ya ki cinyewa musamman a makwannin baya-bayan nan, shuwagabannin kungiyoyin IPMAN da NARTO sun yi karin bayani.
Farashin da fasinjoji masu zirga-zirga a cikin garin Abuja ke biyan direbobi ya tashi sakamakon karancin man fetur da ake fuskanta kamar yadda wasu mazauna babban birnin tarayya Abuja suka bayyana inda direbobin motocin kasuwa ke alakanta tashin farashin da rashin samun mai a gidajen mai suna saya a wajen ‘yan bunburutu a yawancin lokuta.
A wani bangare kuma, hukumar kula da harkokin man fetur ta Najeriya wato fannin Midstream da Downstream ta yi kira ga ‘yan kasar da kada su shiga fargaba da sayan man fetur, tana mai cewa akwai wadataccen mai a kasa.
Idan Ana iya tunawa dai ambaliyar ruwa da aka fuskanta a wasu sassan kasar kamar su jihar Kogi a makwannin baya-bayan nan na daya daga cikin dalilan da su ka jawo matsalar karancin man musamman a birnin Abuja.
Saurari cikakken rahoto daga Halima Abdulrauf: