Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Nijar Sun Zargi Faransa Da Daura Damarar Kai Wa Kasar Hari


Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar
Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar

Sojojin juyin mulkin Jamhuriyar Nijar sun zargi kasar Faransa da soma shirye-shiryen kai farmaki a kasar da hadin gwiwar kungiyar ECOWAS/CEDEAO kamar yadda suka kudiri aniyyar yi a baya da nufin mayar da hambararen shugaban kasa Mohamed Bazoum kan kujerarsa.

A sanarwar da majalisar CNSP ta bayar a kafar talbijan mallakar gwammati a tsakiyar daren Asabar 9 ga watan Satumba wacce Kakakinta Colonel Major Abdourahamane Amadou ya gabatar ta ce daga ranar 1 ga watan nan na Satumba wasu jirage biyu na jigilar sojan Faransa hade da wani kurman jirgi sun sauka a Cote d’ivoire da zummar karfafa matakin da ta sa gaba.

Sannan an girke wasu jirage 2 masu saukar ungulu da motocin soja masu sulke akalla 40 a garuruwan Kandi da Malanville na Jamhuriyar Benin.

Sai kuma a ranar 7 ga watan Satumba wani jirgin sojan ruwan Faransa ya isa Cotonou dauke da dakaru da kayan yaki.

Haka kuma sanarwar ta ce jiragen dakon kaya samfUrin Cargo dauke da lodin kayan yaki sun yi kai da kawo akalla sau 100 a kasashen Senegal Cote d’ivoire da Benin inda suka jibge kayayakin da suka zo da su.

Kawo yanzu Faransar ba ta maida martani ba yayin da ‘yan Nijar suka fara bayyana zullumi akan wannan sabon al’amari.

Majalisar CNSP da gwamnatin rikon kwarya sun yi tur da abin da suka kira manakisa da ke hangen katse hanzarin ‘yan kasa a fafutukar da suka sa gaba danganin Faransa ta kwashe sojojinta daga wannan kasa.

Gaggauta daukan matakai domin zama cikin shirin ta kwana ita ce hanya mafi a’ala a yanayin da ake ciki a yau in ji shugaban gamayyar kungiyoyin farar hula na Reseau Esperanc,e Bachar Maman.

Shugaban kungiyar matasa ta MOJEN Siradji Issa wanda ya jaddada adawarsa da dukkan wani yunkurin amfani da karfin soja a kokarin warware dambarwar siyasar da ta biyo bayan juyin mulkin 26 ga watan Yuli na cewa idan aka hankalci bayanan wannan sanarwa za a fahimci cewa tura ta kai bango a wannan rikici na tsakanin hukumomin Nijar da kasar Faransa.

Sanarwar ta kara da cewa an yi wata ganawa a Damagaran a ranar 1 ga watan Satumba a tsakanin hafsan hafsoshin Nijar da Kwamnan rundunar Faransa a Yankin Sahel don tattauna tsarin ayyukan kwashe dakarun Faransa daga wannan kasa.

Amma kuma kawo yanzu ba abin da aka yi game da wannan aiki lamarin da ke fayyace rashin gaskiyar da ke tattare da wannan kudiri wanda a Zahiri ba na rundunar mayakan Faransa ba ne, haka kuma ba na gwamnatin kasar ba ne.

Majalisar ta CNSP ta tabbatar da cewa dakarun Nijar za su yi tsayin daka don kare martabar kasar da aka gada daga iyaye da kakanni saboda haka ta bukaci al’umma ta ci gaba da jajircewa don cimma nasara a wannan fafutuka ta nuna diyauci.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG