A ranar Talata 12 ga watan Satumba ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta yi kira da a gaggauta sakin wani jami'inta da ke hannun jami'an tsaro a Jamhuriyar Nijar.
Faransa ta ce jami'an tsaron Nijar sun kama wani mai ba Faransa shawara a Nijar a ranar 8 ga watan Satumba.
Jami'in "conseiller des Français de l'étranger" (mai ba da shawara ne ga 'yan kasar Faransa a kasashen waje), wanda zababben jami'i ne wanda ke wakiltar 'yan kasashen waje na Faransa da ke aiki kafada da kafada da ofisoshin jakadancin kasar.
A cewar shafin yanar gizon ma'aikatar harkokin waje, cewa akwai irin wadannan masu ba da shawara guda 442 a duniya. Matsayinsu shi ne taimaka wa ƴan ƙasar Faransa da ke ƙasar waje da batutuwan da suka shafi aiki, makarantu, tsaro na zamantakewa da sauran batutuwa. An zabe su ne na tsawon shekaru shida.
A watan da ya gabata ne dai gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta umarci 'yan sanda da su kori jakadan Faransa daga kasar, a wani matakin da ya kara tsamin dangantaka tsakanin Faransa da kasar da ta yi wa mulkin mallaka. Faransa ta ce hafsoshin sojojin da suka kwace mulki a Yamai a karshen watan Yuli, ba su da hurumin korar jakadan Faransa.
~ Reuters
Dandalin Mu Tattauna