Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

UNGA: Ina Kokarin Sake Maido Da Tsarin Dimokradiyya A Nijar - Bola Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu lokacin da yake jawabinsa a taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78 a binin New York, Amurka
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu lokacin da yake jawabinsa a taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78 a binin New York, Amurka

A jawabin da ya gabatar gaban zauren Majalisar Dinkin Duniya ranar Talata a birnin New York, shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce yana neman sake maido da tsarin dimokradiyya a Nijar don magance matsalolin siyasa da na tattalin arziki da suka dabaibaye makwabciyar kasar bayan juyin mulki.

WAHINGTON, D. C. - Tinubu ya kuma yi maraba da duk wani taimako da zai samu don cimma wannan kudurin.

Tinubu shi ne shugaban babbar kungiyar raya kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS, wadda ke kokarin tattaunawa da gwamnatin mulkin sojan Nijar. Kungiyar ECOWAS ta ce a shirye ta ke ta tura dakaru domin dawo da tsarin dimokradiyya idan kokarin da ake yi ta fuskar diflomasiyya ya ci tura.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu lokacin da yake jawabinsa a taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78 a birnin New York, Amurka
Shugaban Najeriya Bola Tinubu lokacin da yake jawabinsa a taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78 a birnin New York, Amurka

A jawabin nasa a babban taron na shekara-shekara da ake kira UNGA a takaice, Tinubu ya kuma caccaki juye-juyen mulkin da sojoji, wanda ake fuskantar guguwarsa a wasu kasashen yammacin Afirka a ‘yan shekarun nan, kuma wasu lokuta ma ‘yan kasashen da hakan ta faru sukan bayyana farın cikinsu.

"Guguwar da ake gani a sassan Afirka ba yana nuna ana goyon bayan juyin mulki ba ne. wata bukata ce ta magance dadaddun matsaloli," in ji Tinubu.

Taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78 a birnin New York, Amurka
Taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78 a birnin New York, Amurka

“Game da kasar Nijar, muna tattaunawa da shugabannin sojan kasar. A matsayina na shugaban kungiyar ECOWAS, ina so in taimaka wajen sake kafa gwamnatin dimokaradiyya ta hanyar da za a magance kalubalen siyasa da tattalin arziki da kasar ke fuskanta, ciki har da masu tsattsauran ra’ayi da ke neman kawo rashin zaman lafiya a a yankin mu."

Shugaban Najeriya Bola Tinubu a lokacin jawabinsa a taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78 a birnin New York, Amurka
Shugaban Najeriya Bola Tinubu a lokacin jawabinsa a taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78 a birnin New York, Amurka

Matakin da kungiyar ECOWAS ta dauka a watan Agusta na girke dakaru don yiwuwar kai hari ya janyo fargabar karuwar rikici da ka iya kara dagula zaman lafiya a yankin na Sahel da ke fama da tashin hankalin ‘yan ta’adda.

A watan da ya gabata gwamnati sojan Nijar ta umarci dakarunta da su zauna cikin shirin ko-ta-kwana, bisa dalilin karuwar barazanar kai hari.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG