Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Batun Wai Trump Ya Yi Lalata Da Wata Mai Fina-finan Batsa Ya Mamaye Kafofin Labaran Amurka


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Duk da biyan ita Stormy Daniel wasu zunzurutun kudi da lauyan Trump ya yi domin kada maganar ta fito waje lokacin da yake neman zabe, maganar yanzu ta zama ruwan dare gama gari a kafofin labaran Amurka

Labarin lalatar da ake zargin shugaban Amurka Donald Trump yayi da fitacciyar 'yar fina-finan batsa, Stormy Daniel, labari ne da kafofin yada labarai a Washington suka yi makonni da dama da jinsa, tare da yin magana a kai.

Tunda dadewa lauyan shugaba Trump Micheal Cohen ya amince cewa ba shakka sun biya ita Daniel, wadda sunan ta na asali Stephanie Clifford kudi wuri na gugan wuri har dala dubu dari da talatin da niyyar tayi shiru da wannan batu na zargin cewa Trump yayi hulda da ita wato ya neme ta, anyi hakan ne kuma tun kafin ayi zaben shekara ta 2016.

Amma kwaram sai a cikin watan fabarairu ga mujjallar da ake kira In touch ta wallafa hira da wannan matar. Kuma hirar na cike da bayanai filla-filla.

Sai dai duk da yawan karyata wannan labarin dayin shiru bai hana wannan batu yawo a kafofin labarai fitattu dake nan Amurka ba, wanda sai a ranar larabar da ta gabata ne kwaran sai fadar ta White House ta amince da wannan labarin wanda wannan shine karo na farko da suka amince da cewa lallai Trump ya taba hulda da wannan matar.

Sakatariyar yada labarai ta fadar White House Sarah Sander Hukabee a taron manema labarai da aka saba yi a fadar ta White House a kowace ranar Laraba tana kokarin kaucewa wannan tambaya, tana cewa tuni shugaba yayi nasara a kotu game da wannan maganar.

‘’Tace haba tun yaushe shugaba yayi nasara akan wannan magana’’ Sanders tana Magana ne akan umurnin jingine maganar na wucin gadi da kotu ta bayar a cikin satin data gabata, wanda ya baiwa ita Clifford umurnin barin wannan maganar a bainar jamaa game da huldan da suka taba yi da shugaba Trump da kuma hana kai karr shugaban.

Sanders tace ita Cliford ba ta da masaniyar cewa shugaban ya san cewa an biya ta wasu kudade ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG