Rahotanni na bayyana cewa rashin hanyar motar na cikin wani mawuyacin halin lalacewa, lamarin da kan haifar da dogon tsaikon motoci, inda har wasu masu motocin suke kokarin saukewa da rabawa a gefen titin da ke da ramukan gaske.
Mafi akasarin manyan Motocin da ke makare da kaya sun fito ne daga Arewacin Nigeria zuwa kudu yayin da wasu kuma suka fito daga kudancin kasar zuwa Arewa.
Wannan al’amari dai ya jefa jama’a cikin mawuyacin hali na damuwa, sakamakon share kusan kwanaki 3 zuwa 4 a tsaye wuri guda ba tare da sun motsa ba sakamakon toshewar titin baki daya.
Wasu direbobin manyan motocin da lamarin ya rutsa da su, sun bayyana yadda lamarin ya shafi sana’ar su, inda suka yi kira ga gwamnati da gaggauta kai musu dauki.
A lokaci daya kuma wasu direbobin suka yi kiran da a duba yanayin da manyan hanyoyin suke ciki, tare da zimmar gyara su, domin ceto jama’a musamman masu bin hanyoyin daga ukubar da suke fuskantar.
Gwamnan jihar Naija Abubkar Sani Bello ya ziyarci daya daga cikin hanyoyin da suka lalace, wadda ta tashi daga Minna zuwa Suleja, inda ya ce duk da yake hanyoyin mallakar gwamnatin tarayya ne, to amma gwamnatin jihar ta Naija na duba yiwuwar gyara su domin saukaka wa jama’a masu zirga-zirga akan titunan.
Tarihi ya nuna cewa hanyoyin da suka hada kudancin Nigeria da Arewa, an shimfida su ne tun lokacin mulkin soji.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari:
Facebook Forum