Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jonathan Ya Jagoranci Tawaga Zuwa Mali


Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan yayin da suka isa birnin Bamako na Mali. 22, Agusta 2020
Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan yayin da suka isa birnin Bamako na Mali. 22, Agusta 2020

Wakilai daga yammacin Afirka karkashin jagorancin tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, sun isa Bamako, babban birnin kasar Mali a ranar Asabar, a wani mataki na Neman maslaha ga rikicin siyasar kasar da ya kai ga wasu sojoji suka yi juyin mulki.

Tawagar ta yi tattakin ne zuwa kasar domin ganawa da sojojin da suka tilastawa shugaba Ibrahim Boubacar Keita sauka daga mulki a makon da ya gabata, tare da rusa gwamnatin kasar.

Wakilan wadanda suka hada da na kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afirka ta ECOWAS ko CEDEAO, na kuma shirin ganawa da hambararren shugaba Keita tare da wasu jami’an gwamnati da na soji da masu juyin mulkin suke tsare da su.

Ziyarar wannan tawaga na zuwa ne, kwana guda bayan da dubban mutane suka cika a birnin na Bamako domin nuna goyon baya ga sojojin da suka yi boren.

Kasar ta Mali ta sha fama da zanga zangar adawa da gwamnatin Keita, Linda aka yi ta kiraye-kirayen ya sauka daga mulki bayan zaben ‘yan majalisar da aka yi wanda wasu ba su amince da sakamakonsa ba.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG