Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Aka Kama Masu Zanga-zanga a Abuja Da Legas


Yadda aka saka masu zanga-zangar kwantawa a kasa
Yadda aka saka masu zanga-zangar kwantawa a kasa

Rahotanni da ke fitowa daga Najeriya na cewa jami'an tsaro sun tarwatsa tare da kama akalla masu zanga-zanga 60 a birnin Abuja.

Zanga-zangar mai taken #Revolutionnow ya gudana ne a birane da dama a kasar inda suka fito domin zagayowar shekara daya tun da suka yi zanga-zangarsu ta farko a shekarar da ta gabata.

Babban jigon zanga-zangar kuma tsohon dan takarar shugaban kasar Najeriya Omoyele Sowere ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa, jami'an tsaro sun fito suna kokarin muzguna wa wasu masu zanga-zangar a Legas.

A wani sako na daban da shi ma ya wallafa a shafinsa na Twitter, Deji Adeyanju wanda jigo ne shirya zanga-zangar ya bayyana cewa an kama akalla masu zanga-zangar su 60 a birnin Abuja.

Yadda aka saka masu zanga-zangar zama a kasa
Yadda aka saka masu zanga-zangar zama a kasa

Hotuna da bidiyo kan shafukan sada zumunta sun nuna yadda jami'an tsaro suka watsa wa masu zanga-zangar hayaki mai sa hawaye, an kuma ga yadda jami'an suka wuce da wasu masu zanga-zangar a cikin mota.

Jami'an dai har yanzu ba su ce komai game da lamarin ba.

Masu zanga-zangar sun ce sun fito ne domin umartar gwamnati da ta gyara yadda take gudanar da harkokinta.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG